Wata budurwa mai Aljanu ta tashi ajin dalibai a jami’ar Usmanu Danfodiyo

Wata budurwa mai Aljanu ta tashi ajin dalibai a jami’ar Usmanu Danfodiyo

Hankula sun tashi yayin da Aljanun wata daliba suka tashi ana tsaka da darasi a wani ajin dalibai yan aji biyu dake karantar ilimin lissafi a jami’ar Usmanu Danfodiyo, inda kowa ya ranta ana kare, idan baka yi bani wuri, inji rahoton Daily Trust.

A lokacin da Aljanun yarinyar suka tashi, sai aka jiyota tana furta wasu kalamai tare da rikidewa, sai dai a yayin da yan Mazan Ajin ke arcewa, su kuwa kawayenta Mata sun yi ta maza, inda suka dauketa zuwa wajen Ajinnasu.

KU KARANTA: Yan Majalisu zasu binciki Buhari kan zargin nuna son kai a nade naden mukamai

Nan da nan suka kira wani dalibin Ajin masanin Qur’ani, wanda ya tsaya akanta yana yi mata rukiyya, har ta samu kanta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Mutane da dama sun yarda akwai Aljanun da sukan shafi jikin dan Adam, inda idan hakan ya faru zasu dinga tashin masa lokaci zuwa lokaci, sai dai akasarin haka ya fi faruwa da Mata. Itama wata dalibar jami’ar, Aishat Umar ta bayyana cewa ta yi fama da Aljanu a baya.

“Tunanina ya kan gushe, tare da shiga wani hali a duk lokacin da Aljanuna suka tashi, iyayena sun tashi tsaye akaina don samun magani, amma wani gwaji da muka yi a Asibti ya nuna bani da wata matsala, inda likitoci suka tabbatar da cewar Aljanu ne suka shafeni.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel