Mutum miliyan arba'in ne zasu fuskanci barazanar amballiya a kasar nan - Hukumoar Yanayi
- Dumamar yanayi kan shafi miliyyoin mutane a fadin duniya, wanda ayyukan biladama ke haifarwa
- Ambaliyar ruwa ta fara barna a kasar nan daga daminar bana
- Ana hasashen abin zai qazanta ganin yadda daminar tazo ganga-ganga
Bayan da aka maka malelen ruwa a yankuna da yawa na kasar nan, wanda har ya jawo asarar rayuka 50 a jihar Katsina, da ma jikkata da kuma asaarar dukiyoyi da amfanin gona, musamman a sauran jihohi da suka fi amsar ruwan.
Yanzu kuma hukumar Muhalli, karkashin Ma'aikatar Muhalli, ta sanar wa da mataimakin shugaba Buhari, irin ta'annatin da take tsoro daminar bana zata iya yi wa yankunan kasar nan.
Ministan Muhalli, Ibrahim Jibrin yace gwamnati na iya kokarin ta na ganin hakan bai faru ba, amma a hasashe, kashi 20 bisa dari na jama'ar kasar nan su 200m, na fuskantar barazana daga daminar ta bana.
DUBA WANNAN: Zaku sami karin bayani kan karin albashi a banan nan
A dalilan da ya bayar, duk da yace wasu dalilan daga yanayi ne, watau kaddara, sauran dalilai halayyar jama'a kan haiar da ita.
Matsalolin da aka ayyana suna haddasa ambaliya sun hada da, ambaliyar bola, bayan an toshe magudananruwa da ita, gini ba bisa ka'ida ba kan hanyar ruwa, canjawa hanyar ruwa akala, da ma rashin iya tsara birane, duk da zaman 'yan boko da gwamnatoci a kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng