Rayukan Mutane 215 sun salwanta a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun cikin watanni shidda

Rayukan Mutane 215 sun salwanta a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun cikin watanni shidda

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC (Federal Road Safety Corps), ta bayyana cewa kimanin rayukan mutane 215 suka salwanta a sanadiyar afkuwar hadurra a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun tsakanin watan Janairu da Yunin wannan shekara.

Shugaban hukumar na rsehen jihar Legas da Ogun, Mista John Meheux, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin yawan fadakarwa da wayar da kan al'umma a tashar Mota ta Ojota dake birnin Legas.

A cewar sa, an samu afkuwar hadurra 434 akan babbar hanyar cikin watanni shidda da suka gabata inda hadurra 117 suka yi sanadiyar salwantar rayuka.

Rayukan Mutane 215 sun salwanta a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun cikin watanni shidda
Rayukan Mutane 215 sun salwanta a kwararon hanyar Legas zuwa Ogun cikin watanni shidda

Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, an sanya hadurra 237 cikin rukunin mafi muni afkuwa inda mutane 1, 363 suka sha da kyar tare da munanan raunuka.

Legit.ng da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta fahimci cewa, wannan adadi na afkuwar hadurra ta hadar da kimanin mutane 3,696 cikin lokutan da suka afku.

KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta samar da kudaden shiga na N4m a Jihar Oyo

Kwamandan ya kara da cewa, wannan lamari ya tursasa hukumar fara gudanar da yawace-yawacen wayar da kai gadan-gadan musamman a tashoshin Mota domin gargadi direbobi kan hadurra dake tattare da tuki cikin maye da kuma ganganci.

Hakazalika shugaban ya gargadi direbobi kan sanya idanun lura da da kuma kiyayewa musamman a wannan lokuta na damina da ke janyo santsi na titi, rashin kyakkyawan gani da kuma faduwar bishiyu da ka iya janyo barazanar hadurra.

Bugu da kari kwamandan ya shawarci direbobi akan su yawaita zuwa duban lafiyar su kafin daukar hanya ta dogayen tafiye-tafiye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel