Siyasar Kano: Ko a jihar Kano Buhari ya fi karfin Kwankwaso – Sanata Kabiru Gaya
Sanata mai wakiltar yankin Kano ta kudu a majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya ya bayyana cewa babu wani da takarar shugaban kasa da jam’iyyar APC reshen jihar Kano za ta mara ma baya a zaben 2019 face shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gaya ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu a garin Owerri na jihar Imo, a yayin da aka nada shi shugaban kwamitin shirya zaben shuwagabannin APC tun daga mazaba har matakin jiha, inda yake amsa tambaya game da rawar da jam’iyyar APC reshen jihar Kano ke takawa don hana tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ficewa daga cikinta.
KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wata Amarya zuwa Nijar daga Katsina
Inda yace jam’iyyar APC ta jihar Kano na kokarin tafiya da kowa domin a gudu tare a tsira tare, don kuwa babu jam’iyyar dake son wani dan siyasa ya fita daga cikinta, domin a cewarsa ko da kuri’a daya an cin zabe, kuma ana faduwa zabe.
“Amma fa idan burin dan siyasan itace tsayawa takarar shugaban kasa don ya kara da shugaba Muhammadu Buhari, tabbas ba shi da wuri a jam’iyyarmu, don kuwa dan takararmu a jihar Kano shine Buhari.” Inji shi.
Sai dai da aka tambayeshi ko shima yana cikin tsagin APC tawariyya, sai yace “Babu yadda za’ayi ka ganni anan da ina cikin wadancan, don haka ina tare da uwar jam’iyya, suma da suke can zasu dawo, kuma ina da tabbacin Buhari zai lashe zabe.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng