Kotu ta jefa wani Matashi gidan wakafi bisa laifin satar N6, 500 da wayar Salula
Mun samu rahoton cewa wata kotun majistire dake zamanta a birnin Shehu watau jihar Sakkwato, ta garkame wani matashi Aliyu Yaro a gidan kaso bisa laifin satar kudi na kimanin N6, 500 da kuma wayar salula.
Alkalin kotun Nuraddeen Bello, ya bayar da umarnin garkame matashin mai shekaru 24 a duniya domin baiwa hukumar 'yan sanda dama ta gudanar da binciken ta.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, kotu na zargin wannan matashi mazaunin unguwar Kofar Atiku da laifin fashi da makamaki da kuma yiwa jami'an tsaro gardama da ja-in-ja.
Sufeto Samuel Sule, jami'in dan sanda mai shigar da korafi ya shaidawa kotun cewa, Aliyu ya aikata wannan mummunan ta'addanci ne a ranar 21 ga watan Yuni.
KARANTA KUMA: Yadda Kididdigar kasafin kudin zaben 2019 za ta kasance - Buhari
Jami'in dan sandan ya ci gaba da cewa, matashin ya jagorancin wasu mutane hudu inda suka yi tarayya wajen lakadawa wani Hamza Umar dukan tsiya tare da kwacen kudi na kimanin N6, 500 da kuma wayar sa ta salula da darajar ta ta kai N8, 500.
Wannan laifi ya sabawa sashe na 97, 298, 265 da kuma 171 cikin dokar jasa, inda alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng