Rayukan ‘yan bindiga da ‘yan sanda biyu sun salwanta a wani artabu a hanyar Birin Gwari zuwa Funtua

Rayukan ‘yan bindiga da ‘yan sanda biyu sun salwanta a wani artabu a hanyar Birin Gwari zuwa Funtua

‘Yan sanda biyu ne suka rasa rayukansu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai masu hari yayin da suke sintiri a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua a jihar Kaduna.

Kakakin ‘yan sanda a jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu, ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels da hakan a yau, Talata.

A cewarsa, an kaiwa motar sintirin ‘yan sanda harin ne ranar Litinin da daddare a daidai wani kauye da ake kira Tabanni dake karkashin karamar hukumar Birnin-Gwari.

Aliyu ya sanar da cewar wata mata ta rasa ranta bayan wani harsashe ya sameta bisa kuskure.

Rayukan ‘yan bindiga da ‘yan sanda biyu sun salwanta a wani artabu a hanyar Birin Gwari zuwa Funtua
‘yan sandan Najeriya

Kazalika ya bayyana cewar jami’an ‘yan sanda sun kasha biyu daga cikin ‘yan bindigar tare da kwace wata bindiga samfurin AK47 daga wurinsu.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar dakarunta sun sake kwato garin Jilli na jihar Yobe da ‘yan Boko Haram suka kwace ranar daga hannunsu ranar Asabar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Tun bayan dawowarta daga wurin malamin tsibbu take haushin karnuka, in ji mahaifin wata budrwa

Da yake Karin haske a kan harin na garin Jilli, kwamandan soji na Ofireshon lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Roger, ya tabbatar da cewar yanzu haka komai yana karkashin kulawar dakarun soji a yanki da kewayen garin.

Nicholas, ya bayyana harin da cewar abun takaici ne sannan ya kara da cewa faruwar hakan ba sabon abu bane a yanayi na yaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng