Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya

Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kujerar naƙi kan wasu sabbin dokoki hudu da majalisar dokoki ta tarayya ta nemi sahalewar sa tun a ranar 21 ga watan Yunin da ya gabata.

Cikin wata rubutacciyar wasika da shugaban kasar ya aikawa Majalisar ta dattawa inda shugabanta, Dakta Bukola Saraki ya gabatar yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar yau ta Talata.

Legit.ng ta fahimci cewa, sabbin dokokin hudu da majalisar ta nemi sahalewar shugaban kasa sun hadar da ta; kafa cibiyar bayar da kariya ga yara, kayyade da tabbatar da tarar kowane nau'i na laifi, sanya tara kan kowace ma'aikata ko cibiya da ta aikata laifin kisan kai da kuma wata doka kan bayar da bashi ga harkokin noma.

Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya

Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana dalilan sa filla-filla dangane da rashin amincewa da wannan sabbin dokoki da majalisar ta dattawa ta nemi sahalewar sa tun a ranar 21 ga watan Yunin da ya gabata.

KARANTA KUMA: Ronaldo yayi furuci bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

Cikin rubutacciyar wasikar shugaba Buhari ya kafa dalilai tare da dashen hujjojin sa na rashin amincewa, inda ya hikaito wasu dokoki cikin kundin tsarin mulkin kasa da ya sanya ya hau kujerar na ƙi kan wannan sabbin dokoki.

Sai dai daga bisani shugaba Buhari ya rufe wasikar sa da cewa, a shirye yake tsaf wajen bayar da amincewar sa tare da sanya wannan dokoki cikin kundin tsarin kasa muddin majalisar ta yi azamar gyara kurakuran da suka bujuro cikin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel