Rayuka 38, Gidaje 200 sun salwanta cikin wata Ambaliyar Ruwa a jihar Katsina

Rayuka 38, Gidaje 200 sun salwanta cikin wata Ambaliyar Ruwa a jihar Katsina

Kimanin rayukan mutane 38 ne suka salwanta tare da asara ta rushewar gidaje sama da 200 a sanadiyar wata ambaliyar ruwa da ta afku cikin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, ambaliyar ta salwantar da rayukan shanu, tumakai da awakai sama 260 da ta afku a yankunan Kwata, Dantudu, Sabuwa da Tsohuwar Tukare da kuma Unguwar Mai Kwari.

Legit.ng ta fahimci cewa, ruwan saman da ya kece tamkar da bakin kwarya da misalin karfe 11.00 na daren ranar Lahadin da ta gabata har zauwa karfe 1.00 na daren ranar Litinin ya janyo cika da tumbatsar fadamu da koguna da ta yi sanadiyar wannan abin al'ajabi

Cikin mutane 38 da ajali ya katsewa hanzari a sanadiyar ambaliyar ruwan ya hadar har da wata mata mai sayar da abinci, Halima Zubairu Jibia da 'ya'yayen ta biyu da ruwan saman ya ritsa da su cikin bukkar su ta cin kasuwa a yankin Sabon Masallaci.

Rayuka 38, Gidaje 200 sun salwanta cikin wata Ambaliyar Ruwa a jihar Katsina
Rayuka 38, Gidaje 200 sun salwanta cikin wata Ambaliyar Ruwa a jihar Katsina

A yayin tabbatar da wannan lamari cikin wata ganawa da manema labarai ta hanyar wayar tarho, Dagacin Jibia Alhaji Rabe Rabi'u ya bayyana cewa, ambaliyar ta janyo gagarumar ɓarna inda yake rokon gwamnatin akan ta mike tsaye wajen kawo ma su agaji kasancewar lamarin ya dara karfin aljihun su.

Alhaji Aminu Waziri, shugaban cibiyar bayar da agaji na gaggawa ta NEMA, ya gargadi mazauna wannan yankuna akan tabbatar da killacewa tare da zubar da shara a yankunan da suka dace. Ya ce mafi akasarin ambaliyar ruwa tana afkuwa ne a sakamakon toshewar magudanan ruwa.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta cafke wata mata bisa laifin kisan Mijin ta a Jihar Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ziyarci wannan yankuna domin jajintawa al'ummar da ibtila'in ya shafa tare da gudanar da kididdigar girman asara da lamarin ya haifar.

Kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci hukumar ta NEMA akan gaggauta bayar da kayan agaji ga mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa tare da mika sakon ta'aziyyar sa dangane da wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng