Aiki ja: Fadar shugaban kasa ta dorawa Kachikwu alhakin warware rikicin APC kafin 2019
Jam’iyyar APC a jihar Delta ba bayyana cewar fadar shugaban kasa ta umarci karamin ministan man fetur, Dakta Ibe Kachikwu, day a warware rigingimun da jam’iyyar ke fama das u kafin zaben 2019.
Sabon zababben shugaban jam’iyyar APC na Delta, Cif Cyril Ogodo, da jagoran jam’iyyar na jihar, Olorogun O’tega, ne suka sanar da hakan yayin wani taro da suka yi a sakatariyar jam’iyyar dake Asaba, babban birnin jihar Delta, ranar Asabar.
Da yake Magana a wurin taron jam’iyyar, Ogodo ya bayyana cewar shugabancin APC a jihar Delta zai bawa Kachikwu da shugabncin Oshiomhole dukkan goyon bayan da suke bukata domin kawo karshen rikicin da jam’iyyar ke fama da su a jihar.
DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana sirrin nasarar APC a zaben Ekiti
APC na fama rigingimu a jihohi da dama tun bayan kammala zabukan sabbin shugabanni da aka yi a matakin mazabu, kananan hukumomi da kuma jiha.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng