PDP tayi watsi da sakamakon zaben Ekiti, duba hotunan da ta saki a matsayin shaidar magudi
Jam’iyyar PDP tayi watsi da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar na zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi jiya. A sakamakon da INEC ta fitar, dan takarar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, ya sami nasara a kan dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola.
Da sanyin safiyar yau, Lahadi, ne hukumar INEC ta sanar da cewar Fayemi na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11 a cikin 16 dake jihar ta Ekiti. Fayemi ya samu jimillar kuri’u 197,459 yayinda Kolapo ya samu kuri’u 178,121.
Saidai a jawabin da ta fitar ta bakin kakakinta, Kola Ologbondian, ta bayyana cewar an yi masu fashin zabe da tsakar rana tare da yin watsi da sakamakon zaben gabadayansa.
A cewar PDP, sakamakon zaben da suke da shi daga mazabun jihar, ya nuna sune keda mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben amma aka yi amfani da karfin gwamnati da jami’an tsaro aka canja sakamakon zaben.
DUBA WANNAN: Abu 4 da PDP zata yi domin dawo da martabarta a Najeriya - Obasanjo
A wasu jerin sakonni da PDP ta fitar a shafinta dake dandalin sada zumunta na Tuwita ta saki wasu hotuna(kamar yadda ku ka gani a sama) da tayi ikirarin cewar na irin magudin da aka tafka mata ne a zaben na jiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng