Hotunan tsohon shugaba Jonathan a gidan Fani Kayode, leka kuga me ya kaishi
- Matar Fani Kayode ce ta haifa musu'yan uku
- Su Jonathan sun je ziyara da barka
- An dade ba'a ga Jonathan a fili ba
A kwanakin baya ne aka sami qaruwa a gidan tsohon minista dan karadi Fani-Kayode, inda matarsa ta haifo 'yan uku subul.
A baya dai manyan abokai da 'yanuwa sun ta kai ziyara gidan ministan na Abuja, domin sam-barka.
Yanzu dai shima tsohon shugaba Jonathan, da matarsa, sun sami damar kai ziyara gidan tsohon mai kamfe din na mulkin PDP a 2014.
Shugaba Jonathan dai ya sanya albarka, tare da fatan Allah raya ga yaran, wadanda dukkaninsu maza ne.
DUBA WANNAN: Lai Mohammed yayi bayani kan batun satifiket din Kemi Adeosun
Gwamnati ta sanya ido sosai kan kalamai zafafa dake fitowa daga bakin Kayode, wadanda kan tunzura mutane su maida gwamnati kamar bata da iko ko gaskiya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng