Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara ‘yan makaranta

Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara ‘yan makaranta

Dubun wani gardi da ya yi shigar mata don ya saci yara ‘yan makaranta a Ribas ta jihar Fatakwal cika bayan an gano mugun nufin da yake da shi.

Mutanen unguwar Omuchi Igwuruta ne ta garin Fatakwal suka gano mutumin da yanzu haka yana hannun jami’an ‘yan sanda.

Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara ‘yan makaranta
Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara

Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara ‘yan makaranta
Wani gardi ya ci bugu bayan an kama shi da shigar mata yana kokarin satar yara

Wannan ba shine karo na farko da masu satar da mutane da ‘yan fashi ke batar da kama ba domin aikata mummunar sana’ar su. Ko a jiya saida, cikin wata sanarwa da jami'in dan sanda, Abba Kyari, ya fitar, hukumar 'yan sanda ta ankarar da 'yan Najeriya wasu sabbin dabaru da masu garkuwa da mutane da 'yan fashi suka bullo da su na boye bindiga da makamai a cikin injin mota.

DUBA WANNAN: IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

A ranar 9 ga watan Yuli ne sashen hukumar 'yan sanda na IRT (intelligence response team) ya kama wasu 'yan fashi da makami 6 da suka addabi wasu jihohin arewa ta tsakiya.

An kama 'yan fashin ne a jihar Kwara kuma an yi nasarar gano bindigu 4 da alburusai fiye da 500 boye cikin injin motar su kirar Mazda, kamar yadda zaku iya gani cikin faifan bidiyon dake kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel