Buhari da shugaban kasar Afrika ta Kudu sun saka labule a fadar gwamnatin Najeriya, kalli hoto
A yau, Laraba, ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, suka yi wata ganawar sirri a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja.
Shugaba Buhari ya tarbi Ramaphosa bayan isowarsa fadar gwamnatin Najeriya, Villa, da misalign karfe 3:00 na rana.
Shugabannin biyu zasu tattauna batutuwan da suka kasashen da suke shugabanta, musamman batun tattalin arziki da tsaro.
A ranar 8 ga watan Yuli ne fadar shugaban kasa ta koka a kan yawaitar hare-hare da ake kaiwa ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Afrika ta Kudu bisa wasu dalilai marasa ma’ana.
Mai taimkawa shugaba Buhari a bangaren harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana rashin jin dadinta bisa salwantar rayukan ‘yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Yau kuma, Shugaban kasar Namibia ya ziyarci shugaba Buhari
Kamfanin sadarwa na MTN, mallakar kasar Afrika ta Kudu, na fuskantar tirjiya da zanga-zanga daga ma’aikatansu da kungiyar kwadago ta Najeriya a kan rashin mutunta ma’aikata da kulawa da hakkokinsu.
Shugaba Ramaphosa dake ziyarar aiki a Najeriya, zai kasance bako na musamman a taron habaka cinikayya tsakanin kasashen Afrika karo na 25 dake gudana a Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng