Hukumar Soja ta karyata jita - jitar dake nuna cewar zasu dauki sabbin ma'aikata

Hukumar Soja ta karyata jita - jitar dake nuna cewar zasu dauki sabbin ma'aikata

Hukumar sojin Najeriya na shawartar mutane dasu guji duk wata jita jita da zasu ji ba tare da tabbatar daga wurin da ta fito ba

Hukumar Soja ta karyata jita - jitar dake nuna cewar zasu dauki sabbin ma'aikata
Hukumar Soja ta karyata jita - jitar dake nuna cewar zasu dauki sabbin ma'aikata

A wata takarda da Daraktan hulda da jama'a na hukumar soji, Birgediya Janar Texas Chukwu yasa hannu, ya bayyana cewar an jawo hankalin hukumar sojojin Najeriya akan 'yan damfara dake damfarar mutane kudaden su ta hanyar karyar cewa hukumar na diban sabbin ma'aikata.

DUBA WANNAN: Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Takardar ta nuna cewa "Hukumar sojoji tana sanar da cewa diban sabbin ma'aikatan kyauta ne kuma babu wata hanya da ake bukata abi kafin samun shiga aikin.

"Bayan haka kuma hukumar bata fara diban wasu ma'aikata ba, kamar yanda yan damfara ke yadawa a yanar gizo.

"Ana shawartar mutane dasu guji duk wata jita jita da zasu ji ba tare da tabbatar daga wurin da ta fito ba, domin gujewa 'yan damfara da bata gari a cikin al'umma."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng