Cin amana: Wani saurayi ya ari kudin budurwarsa kuma ya auren wata daban ba tare da ta sani ba
- Wata tsaleliyar budurwa ta gamu da ashin tabbas na samarin zamani
- Bayan da ya ranci kudi a gunta ya kuma sanya lalle da wata daban
- Yanzu haka tana asibiti ta fita hayyacinta
Abin al'ajabi baya karewa, wata matashiyar yarinya ta bayyana halin da kawarta ta tsinci kanta bayan yaudara da cin amana da saurayinta yayi mata. Ta bayyana lamarin da abun Allah wadarai inda tace;
"Ya kirata akan ta bashi aron kudi har Naira dubu N650 zai yi amfani da su domin biyan kudin tikitin zuwa birnin Paris dake kasar Faransa domin yin wani kasuwanci".
Kuma haka aka yi, amma ga abin mamaki muna kallon Hotuna a shafin MUA dake intanet kawai sai muka ci karo da hotunan bikinsa da wata mata daban.
KU KARANTA: 'Dan gidan marigayi shugaban kasa ‘Yar Adu’a zai angwance da kyakyawar budurwarsa Saratu Sodangi (Hotuna)
Yanzu haka dai an kwantar da tsohuwar budurwar saurayin a wani asibiti cikin wani mawuyacin hali, wanda sai dai a yi adduar Allah ya bata lafiya.
Faruwar wannan lamari dai ya sanya mutane da yawa tofa albarkacin bakinsu kan maganar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng