Da dumi-dumi: An salami dan sandan da ya kashe yar bautar kasa a Abuja
An salami jami’in dan sanda mai suna, Inspector Benjamin Peters, wanda ya kashe wata yar bautar kasa, Angela Igwetu a Abuja ranan Laraba, 4 ga watan Yuli bayan gurfanar da shi a kotu.
Kwamishanan yan sandan birnin tarayya, Sadiq Bello, ya bayyanawa manema labarai cewa jami’in dan sandan na tsare kuma zai fuskanci gurfana.
Yace bai kamata dan sandan ya harbi motar da yarinyan ke ciki ba, kari da cewa don yarinyan na iwu bai isa hujja ban a harbi.
KU KARANTA: An damke mutane 5 game da kisan yan sanda 7 a Abuja
Bello ya yi bayanin cewa sauran mazaje biyu da ke cikin motan sun bayyanawa masu bincike cewa suna hanyar dawowa daga wani waje ne kawai.
Yace: “Hukumar yan sanda ta dau matakin da ya kamata; an damke dan sandan kuma an kammala shawaran ladabin da za’ayi masa.”
“An sallameshi daga hukumar yan sanda kuma an gurfanar da shi a gaban kotu.”
Yayi kira ga mazauna birnin tarayya da su kwantar da hakulansu saboda hukumar ba zata amince wani daga cikin ma’aikatanta yayi abinda ya ga dama ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng