'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba

'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba

A daren jiya Laraba ne wasu 'yan bindiga da ake zargin yan kabilar Nyandan ne sun hallaka mutane 14 a kauyukan hausawa dake karamar hukumar Lau na jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa kauyukan da aka kai harin sun hada da Santuraki da Abbare da Nnega. Yan bindigan kuma sun kai hari kauyukan Mayo da Lope inda suka kashe Fulani uku kuma suka kona gidaje da dama mallakar hausawa da Fulani.

Harin da yan bindigan suka kai garin Abbare bai yi tasiri ba saboda matasan garin sunyi fio na fito dasu kuma suka samu gallabar a kansu hakan yasa yan bindigar suka koma.

'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba
'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba

DUBA WANNAN: Manomi ya datse hannun makiyayi saboda dabobinsa sun ci masa amfanin gona

Wani mazaunin Abbare, Alhaji Abubakar Abbare ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa babu-gyra-babu dalili yan bindigan suka kawo musu harin, ya kara da cewa mutanen Abbare sun dade suna zaune lafiya da yan kabilar Nyandan.

Abubakar Abbare kuma ya ce yan bindigar sun kone sama da gidaje 40 a rigar Fulani dake arewacin Abbare zuwa wasu kauyukan dake da iyaka da jihar Adamawa, sun kuma sace shanu bayan kone rugogin.

Da yawan al'ummar da aka konawa gidaje sun tare da yan uwansu a Jalingo.

Majiyar Legit.ng kuma ta gano cewa masu ababen hawa sun dena bin titin Mayolope zuwa Numan saboda hare-haren da wasu matasa keyi a hanyar. Masu motocin sun koma bin hanyar Zing-Mayo Belwa.

Kakakin hukumar yan sanda na Taraba, ASP David Misal ya tabbatar da harin sai dai bai fadi adadin mutanen da suka rasa rayyukansu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164