Lokacin ina Matashi na kan kai ziyara Legas gidan wakan Fela – Macron
Mun samu labari cewa Shugaban kasar Faransa na yanzu watau Emmanuel Macron yayi zaman Najeriya a lokacin da yake koyon aiki a ofishin Jakadancin Kasar Faransa da ke cikin Najeriya.
Labari ya kai gare mu daga Gidan yada labarai na CNN cewa Shugaba Emmanuel Macron yayi aiki a babban Birnin Najeriya lokacin yana kokarin sanin bakin aiki. A makon nan ne Shugaban Faransar ya kawo ziyara nan Najeriya.
Bayan nan ma dai Shugaban na Faransa ba bako bane a Najeriya don kuwa ya saba zuwa gidan Marigayi Fitaccen Mawakin nan watau Fela a Legas. Shugaba Macron yace a lokacin yana Matashi yak an leka gidan Mawakin kasar Fela.
KU KARANTA:
Shugaban kasar yayi wannan bayani ne da kan sa ta shafin sa na Tuwita inda yace lokacin yana ‘Dan shekara 23 a Duniya, ya kan kawo ziyara wajen wasan na Fela inda ya nemi sauran ‘Yan uwan sa Turawa su zo su ganewa kan su.
Matashin Shugaban kasar dai ya dawo Birnin Tarayya Abuja wannan karo bayan ya dade da barin kasar. Macron ya zama Shugaban Faransa ne a bara inda ya zama wanda ya fi kowa kankantar shekaru cikin wadanda su ka rike kasar.
Dazu kun ji cewa babban Marubuncin da ake ji da shi a Afrika watau Farfesa Wole Soyinka yayi watsa-watsa da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo. Babban Farfesan na Ingilishi yayi wannan kira ne a wani sabon littafin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng