Girma ya fadi: Yadda malamai ke cinye abincin daliban makarantun Firame a Kaduna
Wata kungiya mai zaman kanta (COGEN) dake bin kwakwafi a kan shirin gwamnatin tarayya na ciyar da daliban makarantun firamare a fadin kasar nan, ta zargi malamai a makarantun Firamaren jihar Kaduna da cinye abincin dalibansu.
Da yake magana a wani taro da kungiyar ta yi a karamar hukmar Jema’a ta jihar Kaduna, shugabar kungiyar COGEN, Rachael Musa , ta bayyana cewar ba dukkan daliban ke samun abincin ba saboda malamansu ne ke cinye mafi yawan abincin.
Rachael ta kara da cewa, duk da gwamnati ta ware cewar za a bawa kowanne dalibi kwai guda daya, kwan bay a isa kowanne dalibi ya samu saboda karanci da ake samu bayan malaman makarantun sun kwashi wani kaso daga ciki.
Kazalika, wani mai saka ido a harkar ciyar da daliban, Monday John, ya zargi ‘yan siyasa da karbar nagoro daga hannun ‘yan kwangilar dake kawo abincin makarantun Firamaren jihar, musamman wadanda suka san ba ‘yan jam’iyyar APC bane.
Mista John ya bayyana cewar, wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun hana ‘ya’yansu cin abincin gwamnatin tarayya bisa zargin cewa yana dauke da guba.
DUBA WANNAN: Nesa ta zo kusa: A karo na farko Jihar Kano ta samu karuwa da jami’a mai zaman kanta
Saidai malaman makarantar sun musanta wannan zargi tare da bayyana cewar abincin da ake kawo masu ne kawai bay a isa, kamar yadda Esther Gushe, mataimakiyar shugaban makarantar Firamaren Aduwan ta sanar da jaridar Daily Nigerian.
Shugaban shirin ciyarwar na karamar hukumar Jema’a, Yakubu Kyari, ya shaidawa New Nigerian cewar yana samun kirat din kwai 300 zuwa 400 sabanin 730 da ya kamata ya samu domin rabawa ga makarantu 177 dake yankin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng