Nigerian news All categories All tags
El-Rufai ya jawo ayoyin Kur’ani domin yi wa al’umma wa’azi kan ji-ta-ji-ta

El-Rufai ya jawo ayoyin Kur’ani domin yi wa al’umma wa’azi kan ji-ta-ji-ta

- Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nemi mutane su guji yada ji-ta-ji-ta

- Nasir El-Rufai yayi amfani da littafi mai tsarki ne domin jawo hankalin jama’a

- Addinin Musulunci ya haramta yada labaran da mutum sam bai ji ba bai gani ba

Mun ji labari cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi wa al’umma wa’azi game da yada ji ta-ji ta inda yayi ruwan ayoyin Al-Kur’ani mai girma domin nuna cewa hakan ba ya cikin koyarwar addinin Musulunci.

El-Rufai ya jawo ayoyin Kur’ani domin yi wa al’umma wa’azi kan ji-ta-ji-ta

Gwamnan Kaduna yayi wa'azi ga masu yada labaran karya

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya koka game da ji ta-ji tan da ake yawo da su a kasar wanda yace su na iya kara jefa Najeriya cikin wani bala’i. Gwamnan yayi wannan bayani ne ta shafin sa na sada zumunta na Facebook kwanan nan.

KU KARANTA: Rayuwar aure: Amfani 3 na auren Macen da ta girmi mutum

Kur’ani dai yayi kira ga Jama’a Musulmai da su bi a hankali wajen yada labarai a Duniya inda aka ce ayi ta-ka-tsan-tsan gudun yin da-na-sani. Littafin mai tsarki dai yayi wannan bayani ne a farkon Sura na 49 watau Suratul Hujurat.

Gwamnan dai ya jawo ayar Kur’anin ne bayan rade-radin karyar da aka yi tayi game da rikicin Fulani da Kabilar Birom a Jihar Filato inda wani ‘Dan jarida ya yada labarin karya na cewa Fulani sun dauki fansa ne kan abin da aka yi masu.

Bincike dai ya nuna cewa sam babu wani Shugaban Fulanin da ya fitar da jawabin da aka yi ta yawo da shi inda ake cewa Fulani sun kashe Birom ne saboda an kashe masu shanu fiye da 300. Rikicin dai ya jawo mutuwar mutane da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel