An tsinci gawawwaki 23 a dajin Zamfara – Rahoto

An tsinci gawawwaki 23 a dajin Zamfara – Rahoto

Rahotanni sun kawo cewa an tsinci gawawwakin mutane 23 a cikin wani daji dake karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara a ranar Juma’an da ta gabata.

Zamfara na daga cikin jihohin arewa dake fama da hare-hare daga barayin shanu da makiyaya, inda hakan ya yi sanadiyan rasa rayuka da kuma lalata dukiyoyi.

Muhammad Shehu, kakakin yan sandan jihar, yace yan sanda sun samu bayanin cewaa an ga gawawwaki a dajin.

A cewar jaridar Daily Trust, wasu daga cikin gawawwakin na dauke da raunukan harbin bindiga sannan wasu kuma na dauke da yankan makogoro.

An rahoto cewa mazauna yankin basu gane fuskokin mutanen ba inda hakan ke nufin bay an yankin bane.

KU KARANTA KUMA: Akwai bukatar mu sake fasalin hukumomin tsaron Najeriya – Makarfi

Wani mazaunin kauyen Boko da ya nemi a boye sunansa yayi ikirarin cewa yan sa kai ne suka kashe mutanen.

An bayyana cewa an binne gawawwakin.

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yayi murabus a matsayin shugaban tsaro na jihar saboda ya kasa shawo kan matsalar tsaro.

Sannan kuma ya bukaci al’umman jihar da su dage da rokon Allah.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng