Ka manta da cin zabe don ko mazabarka ba zaka ci ba – Ganduje ya mayarwa Kwankwaso martini
Gwamnan Kano, Dakta Umar Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba zai ci zabe koda a mazabarsa ba a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.
Ganduje na wadannan kalamai ne a matsayin martini ga kalaman Kwankwaso na cewar zai iya kayar da Buhari idan PDP ta tsayar das hi takarar shugaban kasa a zaben 2019. Kazalika ya bayyana cewar siyasar Kwankwaso a jihar Kano t agama rushewa.
A wani jawabi da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya raba ga manema labarai da yammacin yau, Lahadi, a Kano, Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan ci-ranin siyasa da bashi da basirar iya sarrafa al’amuran Najeriya.
Bayanin na Ganduje ya kara da cewar, “ kalaman Sanata Kwankwaso sun tabbatar da cewar ya rude a siyasance, ya rasa inda zai kama domin bashi da wani tasiri a yanzu.”
“Sama da shekaru 3 Sanata Kwankwaso yana barci a majalisar dattijai ba tare da ya taba gabatar da kudiri ko daya domin kawowa mutanen Kano ta tsakiya cigaba ba. Ko ziyarar mazabarsa bai taba yi bat un bayan zamansa Sanata. Hakan ya nuna cewar bashi da kishin jama’arsa sai cika baki da kuri,” a cewar Ganduje.
DUBA WANNAN: Badakalar Abacha: Kudin ku ya kare - Kasar switherlanda ta sanar da Najeriya
Kazalika, Ganduje ya bayyana cewar, burin Kwankwaso na son yiwa jam’iyyar PDP takarar shugabancin kasa, mafarki ne dab a zai taba zama gaskiya ba saboda mutanen dake cikin jam’iyyar sun san duk karyar sa ta siyasa.
Ganduje ya kafe kan cewar Kwankwaso bashi da ragowar wani tasiri a siyasar Kano kuma zai karasa rugurguza shi a zaben 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng