Masana sun ce akwai fa’ida kwarai mace ta girmi mijin ta na aure

Masana sun ce akwai fa’ida kwarai mace ta girmi mijin ta na aure

Wannan karo kuma mun kawo maku wasu amfani na ace namiji ya auri Macen da ta girmi sa. Ko da dai hakan wani abu ne da ba a saba gani a irin wannan Yankunan amma kuma sam ba aibu bane har a addini.

Masana zaman aure da kiwon lafiya da masu karantar halayya da dabi’a sun ce akwai amfanin mace ta girmi mijin ta. Daga cikin amfanin da ake fada dai akwai:

1. Rashin yarinta da wasa da hankali

Idan har mutum yayi dace da mace da ta grime sa, to ya huta da yarinta da duk wani shirme a wajen zaman aure. A lokacin da mace ta kai wasu shekaru dai za a same ta duk ta ajiye kallabin wasa da hankalin namiji.

KU KARANTA: Wata mata ta aika mijin ta na aure lahira a Zamfara

2. Samun abokiyar shawara

Idan namiji ya samu mace mai shekaru yayi dace da abokiyar shawarar sa a rayuwa. Dalili kuwa shi ne ta san rayuwa saboda dadewar da tayi ana gogawa da ita. Wadanda su ka riki matan su abin shawara kuwa su na samun nasara a rayuwa.

3. Iya kwanciyar aure

Masana har wa yau sun nuna cewa manyan mata sun fi sanin harkar zaman daki da tarawa a aure. Manyan mata sun kuma fi rashin kyashi. Dama dai ana cewa mai son girki ya auri budurwa amma kuma mai son kwanciya sai ya nemi babbar mace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng