Har ila yau: Gobarar iskar gas ta kone shaguna 15 a Kaduna, an fattaki jami’an hukumar kashe gobara

Har ila yau: Gobarar iskar gas ta kone shaguna 15 a Kaduna, an fattaki jami’an hukumar kashe gobara

Wata gobara da ta tashi sakamakon fashewar sinadarin iskar gas da yammacin jiya, Asabar, a garin Kaduna tayi sanadiyar konewar shaguna 15 tare da raunata 15.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar lamarin ya faru ne da misalign karfe 5:40 na yammacin Asabar a Iayin Ibrahim Taiwo dake kan titin Ibrahim Taiwo a garin Kaduna.

NAN ta rawaito cewar mazauna layin ne suka yi gangami tare da kashe gobarar kafin tan yadu ya zuwa wasu sassan layin.

Kazalika, NAN ta rawaito cewar shagunan sayar da kayan dakin girki ne gobarar ta fi shafa a layin na Ibrahim Taiwo dake da cunkuson jama’a.

Har ila yau: Gobarar iskar gas ta kone shaguna 15 a Kaduna, an fattaki jami’an hukumar kashe gobara
Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa'i

Mazauna layin sun kori jami’an hukumar kashe gobara da suka zo daga jami’ar jihar Kaduna, sa’a guda bayan tashin gobarar.

Wani daga cikin masu shaguna a layin, Ifeanyi Eze, ya shaidawa NAN cewar gobar ta tashi ne sakamakon haduwar wayar wutar lantarki a shagon da ake sana’ar sayar da tukunya da iskar gas.

Wani shaidar gani da ido, Samuel Emma, y ace wutar ta fara ci daga daga shagon da ake harkar iskar gas bayan wata kara mai karfi, sakamakon fashewar tukwanen iskar gas.

DUBA WANNAN: Gobarar tankar dakon mai a Legas na daga cikin manyan da suka samu Najeriya - Buhari

Da suke bayyana dalilin korar ma’aikatan hukumar kashe gobara, wani mazaunin layin na Ibrahim Taiwo, Hamza Ado, ya bayyana cewar saida suka kira jami’an hukumar lokacin da gobara ta fara amma basu zo ba sai bayan fiye da sa’a guda lokacin da tuni sun kasha wutar.

Kazalika, mazaunan layin sun yi godiya ga ubangiji kasancewar babu asarar rai sakamakon gobarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng