Hukumar 'Yan sanda ta cafke wasu 'yan ta'adda 2 a jihar Zamfara
Hukumar 'yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke wani shahararren dan fashi da makami da ta sakaya sunan sa a garim Gurusu dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, shine ya bayyana hakan a birnin Gusau cikin wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata.
Shehu yake cewa, hukumar ta samu wannan babbar nasara ne a ranar Juma'ar da ta gabata sakamakon wani rahoto da ta samu na cewar 'yan ta'adda na kai komo a yankin.
Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar'yan sanda ta samu nasarar cafke wannan shu'umin mutum tare da hadi gwiwar reshen ta na garin Anka, inda ta gudanar da wani sintiri tare da ran-gadi har na tsawon sa'o'i hudu da har sai da hakar ta ta cimma ruwa.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na najeriya ya ruwaito, hukumar ta kuma damke wannan dan ta'dda tare da bindiga da alburusai masu tarin yawa.
DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga sun sace Shanu 9, sun kashe mutum 1 a jihar Filato
A yayin haka kuma, hukumar ta cafke wata Mata, Salamatu Shehu a kauyen Rafin-Gona dake yankin karamar Anka bisa laifin kashe mijinta.
Lamarin ya afku ne a ranar 27 ga watan Yuni inda wannan mata ta salwantar da rayuwar mijin ta yayin da rashin jituwa ta shiga tsakanin su da ya sanya ta rade shi da katako.
A cewar sa, a halin yanzu hukumar tana ci gaba da tattara bincike domin gurfanar da wannan 'yan ta'adda a gaban Kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng