Adamawa 2019: Murtala Nyako da Babachir sun ingizo Nuhu Ribadu ya fito takarar Gwamna
A yayin da zabukan gama gari na shekarar 2019 cigaba da karatowa, yan siyasa na ta shirya dabaru daban daban da suka ganin zasu kaisu ga gaci, wanda suke ganin idan kuma aka samu akasin kulle kullensu, tabbas za’a kaisu kushewa a siyasance.
Wasu jigogi a tafiyar siyasar bakar hula dake daukat hankali a jihar Adamawa, da suka hada da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da tsoho sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal sun yi kira ga tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu da ya fito takarar gwamnan jihar.
KU KARANTA: Koyarwar addinin Musulunci: Labarin wani Limami a garin Jos da ya boye Kiristoci a cikin Masallaci
Jiga jigan sun yi wannan kira ne a yayin wata ziyara da suka kai ma Ribadu a gidansa dake garin Yola, inda suka bukaceshi da ya fito takarar gwamna don ya kawar da gwamnatin gwamna Bindow Jibrilla, hakan ne kadai zai tabbatar da canjin da suke bukata a jihar.
Kaakakin tafiyar Bakar hula, Salau Amada ya bayyana cewa sun yi kira ga Ribadu da ya bayyana takararsa da wuri saboda sunan da yake da shi a Duniya tun a zamanin da ya rike EFCC, tare da kwarewa da sanin makamin aiki.
A nasa jawabin, Ribadu ya bayyana godiyarsa da goyon bayan da suke nuna masa, tare da yabo da yake sha daga jama’an gari, sa’annan yayi alkawarin tabbatar da tsaro a jihar idan har ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng