Najeriya ce kasa ta 9 mafi hatsari ga mata – Rahoto
Sabon rahoto da gidauniyar Reuters Foundation ta saki a ranar Talata, ya ambaci Najeriya a matsayin ta tara cikin kasashe mafi hatsari ga mata.
Najeriya ta shiga rukunin tare da Iniya wacce itace kan gaba a jerin kasashen, DR Congo, Saudiyya, Afghanistan, da kuma Somalia ta fannin lalata, tsubbu da kuma safarar mutane.
Sauran kasancen dake da rahoto mara kyau ta fannin kula da mata sun hada da Amurka, wacce ta kasance ta karshe a rukunin, Syria, Pakistan da kuma Yemen.
Tsakanin ranar 26 ga watan Maris da 4 ga watan Mayu, 2018 gidauniyar Thomson Reuters Foundation sun watsa kwararru 548 kan lamuran mata a fadin duniya, wanda suka hada da fannin ilimi, ma’aikatan lafiya, masu shirya manfofi da kuma ma’aikatan NGO.
KU KARANTA KUMA: Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari
An bukaci wakilan da su lura da bangarorin: lafiya, al’addu, tozarci, lalata da kuma safarar mutane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng