Ba labari! Wani tsohon Soja ya harbe kansa har lahira
- Abin ba kyau, ko me yayi zafi har ta kai ga ya kashe kansa?
- Wani tsohon sojan Najeriya ne ya harbe kansa bayan dawowa daga farauta
- Har ya zuwa yanzu dai ba'a kai ga gano dalilin daukar wannan mummunan matakin ba
Yanzu haka dai wani rahoto ya bayyana cewa wani tsoho mai shekaru 70 mai suna Boluwaji Adenugba ya harbe kansa har lahira ta hanyar amfani da bindigar farauta a garin Ore na jihar Ondo.
Rahotannin sun bayyana cewa mamacin tsohon Jami'in sojan kasar nan ne, kuma ya aikata wannan ɗanyen aiki ne jim kadan bayan dawowarsa gida daga farauta a ranar Talatar da ta gabata.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu wani cikakken bayani game da dalilin da yasa ya aikata hakan ba, sai dai wani mutum daga cikin mazauna kauyen yace watakila hakan ya faru ne sakamakon saɓani da ya samu da daya daga cikin 'ya'yansa mata.
KU KARANTA: Dubu ta cika: Wadansu da suka yiwa gawa fyade sannan suka gasa namanta suka cinye sun shiga hannu
Ya ce "Sun samu sabani da 'yarsa har ya kai su ga cacar baki wanda hakan ya fusata shi ya shiga daki ya rufe kofarsa ta baya. Jim kadan kuma sai ya harbe kansa da bindigar da take tare da shi".
"Ƙarar harbin da makota suka ji shi yasa suka rankaya da gudu domin ganin abinda yake faruwa, ko da aka bude kofa sai jama'a suka same shi kwance jikin jini rai yayi halinsa".
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce "Yanzu haka muna cigaba da bincike domin sanin abinda dalilin da yasa ya aikata hakan"
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng