Mata da ‘ya’yan wani dan sanda sun bawa ‘yan ta’adda kwangilar kashe shi

Mata da ‘ya’yan wani dan sanda sun bawa ‘yan ta’adda kwangilar kashe shi

Ana tuhumar wata mata da ‘ya’ya hudu na wani dan sandan kasar Indiya da bawa wasu ‘yan ta’adda kwangilar kashe shi domin mallake kudin na fansho, $115.91, da aka ba shi.

Kazalika sun bayyana cewar, wani dalili da ya sa suka bayar da kwangilar kasha shi shine; ya hana su saka wando.

An samu gawar dan sandan, Meharbaan Ali, mai mukamin mataimakin Insifekta, ranar Lahadi yashe cikin wani babban bututun gudanarwar dagwalo dake da nisan mita 50 kacal daga gidan sa a garin Pradesh, dake arewacin kasar Indiya, kamar yadda Daily Mail ta wallafa.

Mata da ‘ya’yan wani dan sanda sun bawa ‘yan ta’adda kwangilar kashe shi
'Yan sandan kasar Indiya

‘Yan sanda sun kama matar marigayi Ali, Zahida Begum; mai sheklaru 52 a duniya, da ‘ya’yanta: Saba, shekaru 26; Zeenat, shekaru 22; Iram, shekaru 19; da Alia, shekaru 18, a gidan su dake Shahjahanpur bayan sun amsa laifin su da bakinsu.

DUBA WANNAN: An kama malamin addini da laifin kisan wata karuwa domin yin tsatsiba, duba hotuna

Bayan an tsinci gawar marigayi Ali ne sai ‘yan sanda suka fara bincike. Kuma sun yi nasarar gano cewar da hannun iyalinsa ne ta hanyar na’urorin tsegumi dake makale a gefen tituna.

Dan sanda mai bincike, Insifekta Daya Chand Sharma, na ofishin hukumar ‘yan sanda dake Bazaar, ya bayyana cewar iyalin Ali sun kasha shi ne saboda tsaurin da yake nunawa a kan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng