'Yan sanda sun tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a jihar Jigawa

'Yan sanda sun tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a jihar Jigawa

Hukumar 'yan sanda ta jihar Jigawa, ta tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a duniya cikin dokar wani daji dake karamar hukumar Dutse ta jihar kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito a ranar Talatar da gabata.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Abdu Jinjiri, shine ya bayar da tabbacin wannan lamari a ranar Talatar da gabata yayin ganawa da manema labarai a birnin Duste.

Jinjiri ya bayyana cewa, bincike ya tabbatar da wannan Mata mai sunan Sahura Shua'ibu, an tsinton gawar ta ne da misalin karfe 9.00 na daren ranar Lahadin da ta gabata cikin kauyen Bukki dake karamar hukumar ta Dutse.

Legit.ng ta fahimci cewa, ta samu nasarar gano wannan gawa ne ta Marigayiya Sahura a sakamakon rahoton wani Mallam Musa Ado na kauyan Warwade da ya ankarar da jami'an na tsaro.

'Yan sanda sun tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a jihar Jigawa
'Yan sanda sun tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a jihar Jigawa

A yayin kacibus da wannan rahoto ne jami'an suka dirfafa kauyen inda suka riski gawar kwance cikin dokar daji kamar yadda kakakin 'yan sandan ya bayyana.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Jihar Gombe ta bayar da tallafin N10m da Kayan agaji ga wadanda bala'in Bauchi ya shafa

A cewar sa, ana zargin an yi amfani da kotar fatanya ne wajen rade wannan Mata da yayin da aka rsike ta da har ya yi sanadiyar mutuwar ta.

A halin yanzu dai an mika gawar wannan Mata zuwa babban Asibitin garin Dutse domin kwararrun Likitoci su gudanar da bincike akan ta wajen gano ainihin musabbabin Muturwa ta, a yayin da suke ci gaba da bincike domin bankado wadanda suka aikata wannan mummunan ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel