Yadda Sarki Muhammadu Sunusi II ya kaddamar da aikin kankare titin Abuja zuwa Kano
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ne ya jagoranci bikin kaddamar da sake gin babbar hanyar da ta taso daga garin Abuja zuwa jihar Kano, kamar yadda gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an yi bikin kaddamar da aikin ne a ranar Talata, 26 ga watan Yuni, kuma hanyar za ta ratsa garin Kaduna, ta dauka har zuwa jihar Kano, kuma ya samu halartar Sarkin Kano, mataimakin gwamnan jihar Kano, Sanatoci, kwamishinoni daga jihohin Kaduna da Kano.
KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi jarumta wajen tartwatsa gugun yan fashi da makami
A farkon shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada kwangilar gudanar da aikin kankare tsohon lalataccen titin Abuja zuwa Kano, tare da shimfida sabon kwalta, da kuma fadada hanyar.
Da yake aikin babba ne, an kasashi zuwa kasha uku, kashin farko zai taso daga garin Zuba na babban birnin tarayya Abuja, zuwa babbar hanyar jihar Kaduna, watau Kaduna Western Bye pass, wanda tsawonsa ya kai kilomita 165.
Bidiyon:
Kashi na biyu ta fara daga gadar Kawo zuwa garin Zaria, tsawonsa kilomita 73.4, sai kuma kashi na uku da ya fara daga garin Zaria zuwa jihar Kano. Ana sa ran kammala aikin cikin shekara daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng