Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya

Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya

Jam'iyyar APC ta tabbatar da tsohon shugaban kungiyar kwadago na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole a matsayin sabon zababen shugaban ta na kasa.

Mr Oshiomole ya yi nasarar zama sabon shugaban jam'iyyar ne cikin sauki saboda dukkan sauran abokan takararsa sun janye.

Kazalika haka ragowar shugabannin jam'iyyar 11 aka zabe su ba tare da abokan hamayya ba, ta hanyar yin sulhu tsakanin masu takarar kujeru daban-daban. Ga jerin sunayen su da mukaman su;

1. Ibrahim Masari, Sakataren walwala.

2. Tunde Bello, Sakataren kudi.

Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya
Osinbajo, Buhari da Oyegun a wurin taron zaben shugabnnin APC

3. Zakari Mohammed, Sakataren jam'iyya na yankin arewa ta tsakiya.

4. Hassana Abdullahi, Shugabar mata ta yankin arewa ta tsakiya.

5. Nelson Abba, Ex-officio na yankin arewa ta tsakiya.

6. Abubabakr Ajiya, Sakataren jam'iyya na yankin arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

7. Isa Azare, Ex-officio na yankin arewa maso gabas.

8. Tukur Gusau, Sakataren jam'iyya na yankin arewa maso yamma

9. Nasiru Haladu, Ex-officio na yankin arewa maso yamma

10. Mrs Rachael Akpabio, Shugabar mata ta yankin arewa ta kudu maso kudu

11. Misbahu L Didi, Wakilin masu bukata ta musamman

Da akwai yiwuwar ta hanyar sulhu za a fitar da ragowar shugabannin jam'iyyar 42 kamar yadda aka sanar da wadannan ya zuwa yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng