Abubuwa 4 da za su iya hana PDP tsayar da Sule Lamido

Abubuwa 4 da za su iya hana PDP tsayar da Sule Lamido

Sule Lamido, tsohon minista kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, na daga cikin 'yan siyasar Najeriya da sunan su ya ratsa ko ina kuma suka dade suna gwagwarmaya.

A yanzu haka Lamido na daga cikin 'yan siyasar dake burin fatan ganin jam'iyyar sa ta PDP ta tsayar da su takarar shugabancin kasa domin fafatawa da shugaba Buhari a zaben 2019. Saidai a wani nazari na siyasar Najeriya da kuma halin da Lamido ya tsinci kan sa da yawan jama'a na ganin zai yi wuya ya samu sahalewar jam'iyyar sa domin zamar mata dan takara a zaben 2019. Ga wasu daga cikin kalubalen da yake fuskanta.

1. Shari'a da EFCC bisa zargin sa da badakala

Ba boyayyen abu bane cewar Lamido na fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) bisa zargin sa da almundahana da kudin mutanen jihar Jigawa. Wani abu da ya kara dagula batun tuhumar da EFCC ke yiwa Lamido shine har da 'ya'yan cikin sa ake tuhuma.

2. Rashin alaka mai kyau da jagororin jam'iyyar PDP

Wasu na ganin cewar babu alaka mai kyau tsakanin Lamido da jagororin jam'iyyar PDP musamman gwamnoni da kuma tsohon shugaban kasa Jonathan.

Abubuwa biyar da za su iya hana PDP tsayar da Sule Lamido
Sule Lamido

3. Nuna izza da iko ga jama'a

Masu sharhin siyasa sun tabbatar da cewar Lamido mutum ne mai son nuna iko da gadara a harkokin sa. Masu sharhin na ganin cewar Lamido na nuna tsageranci ta hanyar nuna bashi da wani ubangida ko kuma wani wanda zai tankwara shi a kan ra'ayin sa.

4. Rashin tabbas a kan farinjini da karbuwar sa a arewa

Kokarin jam'iyyar PDP shine ta tsayar da wani dan takara da zai iya samun mafi rinjayen kuri'un arewacin Najeriya, yankin da shugaba Buhari ya fito.

DUBA WANNAN: Ni ma zan fito takarar shugaban kasa a APC – wani Sanata daga arewacin Najeriya

Shugaba Buhari har yanzu yana da masoya da magoya baya masu dumbin yawa a arewa sannan ga karfin iko dake hannun sa da kuma goyon bayan gwamnonin jihohin arewa da kusan dukkan su 'yan jam'iyyar APC ne.

Bayan suna da ya yi a matsayin sa na dan siyasa, jam'iyyar PDP ba ta da tabbacin cewar mutanen arewa zasu bawa Lamido goyon baya kamar yadda suke bawa shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel