Yadda tsananin gwale-gwale a wata makarantar sakandire ke neman nakasta wata karamar yarinya

Yadda tsananin gwale-gwale a wata makarantar sakandire ke neman nakasta wata karamar yarinya

Wata karamar yarinya mai shekaru 13 a duniya dake karatu a wata makarantar sakandire ta Sheikh Abdulkadir dake garin Ilorin na jihar Kwara ta samu gurdewar kasha a kafar ta bayan an yi mata horo da tsallen kwado mai tsanani sakamakon zuwa makaranta a makare.

Yarinyar, Suliat Ganiyu, ta gamu da wannan tsautsayi na gurdewa a kafa a cikin watan Fabrairu bayan wani malami a makarantar ya umarce tad a yin tsallen kwado saboda ta zo a makare, kuma tana cikin tsallen kwadon ne sai kashin tan a kafa ya gurde.

Gurdewar dalibar, Suliat, ta kara rincabewa bayan shigar wasu kwayoyin cuta cikin jikinta a daidai wurin da ta samu rauni bayan kashin kafar ta ya gurde.

Yadda tsananin gwale-gwale a wata makarantar sakandire ke neman nakasta wata karamar yarinya
Suliat, Ministan Ilimi

Jaridar Punch ta rawaito cewar, yarinyar na zaune ne da wata ‘yar uwar ta, kuma ta shaidawa wakilin jaridar cewar, sun gano ta samu gocewar kashin ne bayan tayi korafin matsanancin ciwon kafa bayan dawowar ta daga makaranta. Daga bisani ta shaidawa ‘yar uwar ta cewar ta samu ciwon ne sakamakon tsallen kwado da malamin ta ya saka ta.

DUBA WANNAN: Bashi da wani tasiri a siyasar Kano – Ganduje ya yi tone-tone a kan rikicin sa da Kwankwaso

Da yake ganawa da wakilin jaridar Punch, wani dan uwa ga Suliat mai suna Saheed y ace sun sanar da ma’aikatar ilimin jihar Kwara abinda ya faru kuma ta umarci hukumar makarantar ta dauki dawainiyar biyan kudin magunguna da aikin gyaran kafar, umarnin da suka ce har yanzu shugaban makarantar bai yiwa biyayya ba.

Yanzu haka likitoci sun yi barazanar cewar yarinyar kan iya rasa kafar da ta samu matsalar matukar ba a gaggauta yi maka aiki da zai lakume kudi, N250,000 ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng