An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya

An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya

A yau Laraba ne kotun tarayya da ke Legas ta fara sauraran karar Peter Nwaoboshi, Sanatan jam'iyyar PDP da ake tuhuma da laifuka biyu masu alaka da makirci da almundahar kudade atre da gabatar da shedu biyu.

Hukumar yaki masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC ta tsare sanatan na wasu kwanaki kafin daga baya alkalin da ke sharia'ar Mohammed Idris ya bayar da belinsa.

An tuhumar sanatan a kan laifukan guda biyu tare da wasu kamfanoni guda biyu; Golden Touch Construction Project Limited da kuma Suiming Electricals Limited.

An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya
An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya

KU KARANTA: Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

Laifi na farko da ake tuhumar Sanatan shine sayar wani gida mai suna Guinea House da ke Marine Road a Apapa Legas a kan kudi N805 miliyan a cikin watan Mayu da Yunin 2014 ba bisa ka'ida ba.

Lauya mai shigar da kara ya ce sanatan ya dace ya sani cewa N322 miliyan cikin kudin sayan gidan kudade ne da aka mallake su ta hanyar haram.

Laifin ne biyu da ake tuhumarsa kuma shine yin amfani da kamfanin safarar kayayakin lantarki na Golden Touch Construction Projects Limited wajen karkatar da kudaden gwamnati.

A wata labarin Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018 a fadar sa ta Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Rashin sa hannu a kan kasafin kudin ne dama ya ke kawo tsaiko wajen fara wasu ayyukan gwamnati amma yanzu ana sa ran za'a fara gudanar da ayyuka da dama kuma talakawa zasu fara morar romon demkradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel