Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci hare-haren ƙunar bakin wake na Damboa

Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci hare-haren ƙunar bakin wake na Damboa

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana mai jagorancin gudanar da agaji da jin kai ta majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Ms Myrta Kaulard, ta la'anci afkuwar hare-haren kunar bakin wake a Jihar Borno na ranar Asabar din da ta gabata.

Wannan hari kamar yadda rahotanni suka bayyana ya salwantar da rayuka masu dumbin yawa tare da munanan raunuka da ya gadar wa mutane da dama a jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Kasar nan.

Harin na garin Damboa ya kasance daya daga cikin mafi munin afkuwa a tarihin garin kamar yadda Ms Myrta ta bayyana cikin wata sanarwa a babban birnin kasar nan na tarayya da sanadin kakakin ta, Mista Abiodun Banire.

A sanadiyar haka ne Ms Myrta take mika sakon ta na gaisuwa da ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya salwantar da rayuwar 'yan uwan su tare da fata samun waraka cikin gaggawa ga wadanda suka raunata.

Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci hare-haren ƙunar bakin wake na Damboa
Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci hare-haren ƙunar bakin wake na Damboa

Hakazalika ta na kuma mika sokon ta na ta'aziyya ga gwamnati da kuma daukacin al'ummar Najeriya baki daya tare da neman juriyar su dangane da wannan abin bakin ciki da ya afku.

KARANTA KUMA: Mutane 2 sun jikkata yayin da 'yan Baranda suka gwabza a Birnin Dutse

Ta kara da cewa, rayukan mutane sama da 200 da suka hadar da kowane jinsi da babu babba babu yaro sun salwanta a ire-iren wannan afkuwa ta munanan hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tun gabanin shekarar nan musamman na garin Mubi a jihar Adamawa.

Legit.ng ta fahimci cewa, wakiliyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma nemi gwamnatin Najeriya akan ta kara kaimi wajen bai wa al'ummar ta tsare rayukan su gami da Lafiya da kuma Dukiya.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Katsina AMinu Bello Masari, ya sha alwashin bayyana cikakken lissafi na adadin kudade da gwamnatin sa ta batar wajen gudanar da al'amurran jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel