Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari a jihar Kano

Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari a jihar Kano

A ranar Lahadi 17 ga watan Yuni, wani magidanci da iyalansa sun gamu da ajalinsu sanadiyan hatsarin mota day a cika da su.

Mutumin da aka ambata da suna Kamalu, na tare da matarsa Surayya da 'ya'yansu biyu 'yan mata, daya mai shekara biyu daya kuma mai wata takwas.

Sun fito daga ne yankin Maidile inda za su yankin unguwa Uku gidan iyayen matar a garin Kano domin yin gaisuwar Sallah cikin wata a daidaita sahu a lokacin da hatsarin ya faru.

Sun isa daidai Western Bypass sai wata babbar mota tirela ta bi ta kan keken da suke ciki.

KU KARANTA KUMA: Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya

A sanadiyyar hatsarin dukkan iyalan gida dayan suka mutu nan take har da direban keken.

A baya munji cewa, karo na biyu cikin kwanaki bakwai kacal, an kara samun wani matashin daga kasar Bangladesh da ya sake kashe kan sa a masallaci mai alfarma na garin Makka a cikin satin da ya gabata kamar dai yadda muka samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng