Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya

Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya

- Mai rikon kwaryar ofishin darektan yada labarai na hukumar soji, Birgediya John Agim, ya mayar wa gwamnatin jihar Taraba martani a kan yin watsi da rahoton binciken zargin da TY Danjuma ya yiwa sojin

- Ya bayyanar cewar gwamnatin jiharb ta ki amincewa a kwace makamai daga hannun jama’a saboda ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin dalilan siyasa.

- Agim ya kafe kan cewar dakarun soji basu taba arangama da makiyaya ba a jihar duk da kasancewar rundunar sojin dake aiki na jihar ne

Mai rikon kwaryar ofishin darektan yada labarai na hukumar soji, Birgediya John Agim, ya mayar wa gwamnatin jihar Taraba martani a kan yin watsi da rahoton binciken zargin da TY Danjuma ya yiwa sojin na taimakon makiyaya a rikicin dake faruwa a jihar ba.

Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya
Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya

Da yake hira da jaridar Punch, Agim ya bayyanar cewar gwamnatin jiharb ta ki amincewa ta bawa hukumar soji hadin kai domin a kwace makamai daga hannun farar hula saboda ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin kashe jama’ar da basa goyon bayan su.

DUBA WANNAN: “Zan so na sace shi zuwa APC “ –Shugaba Buhari ya na son ganin wani sanatan PDP ya koma APC

Agim ya kafe kan cewar dakarun soji basu taba arangama da makiyaya ba a jihar duk da kasancewar rundunar sojin dake aiki na jihar ne tare da bayyana cewar gwamnatin jihar da hukumar sojin sun fara samun sabani ne tun bayan da dakarun soji suka ki yarda da zama rakumi da akala a hannun ‘yan siyasa.

Sannan ya kara da cewa sun sha kama matasa masu nasaba da ‘yan siyasa da makamai amma basu fitar da rahotannin hakan ba saboda basa son a fassara shi ta fuskar siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng