Goron Sallah ga 'yan fursunan jihar Kano, leka kuji me gwamna ya yi musu

Goron Sallah ga 'yan fursunan jihar Kano, leka kuji me gwamna ya yi musu

- Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano yana daya daga cikin magoya bayan shugaba Buhari na keke-da-keke

- Gwamnan yana amfani da duk damar da ya samu na yin magana wajen yiwa shugaba Muhammadu Buhari kamfen

- Gwamnan ya sake aikata hakan yayin da ya saki wasu fursunoni 317 daga gidan yari daban-daban na Jihar

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya saki wasu fursunoni 317 daga gidan yari daban-daban na Jihar kana ya bukace su da suyi wa shugaba Muhammadu Buhari addua'a kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ganduje ya ziyarci gidajen yari na Kano Central da Kurmawa da Goron Dutse duk a ranar Juma'a a yunkurinsa na ziyarar mutanen da ke bukatar kulawa a jihar, kana ya saki wasu daga cikin fursunonin bayan anyi musu afuwa.

Ganduje ya saki fursunoni 317, ya ce su yiwa Buhari addua'ar nasarar lashe zabe
Ganduje ya saki fursunoni 317, ya ce su yiwa Buhari addua'ar nasarar lashe zabe

Ya yi kira ga tsaffin fursunonin da su canja halayen su kana ya bukaci su yiwa shugaba Muhammadu Buhari addu'a don Allah ya kare shi daga sharin "wadanda suke son ganin bayansa."

Ya ce: "Ina bukatar ku yiwa shugaba Muhammadu Buhari addu'a Allah ya kare shi saboda ya tsallake sharri mutanen da ke kokarin lalata mana kasa ta hanyar rashawa da cin hanci.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan gwamnoni su taimaka wajen rage cinkoso a gidajen yarin da ke jihohinsu. Muna aikata abinda shugaban kasa ya umurce mu da yi ne."

Wasu daga cikin fursononin da aka saki sunyi jawabi a ziyarar inda suka mika godiyansu ga Gwamna Ganduje saboda ya ceto su.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaban gidajen yari na Jihar Kano, Magaji Abdullahi ya yabawa gwamna Ganduje kasancewarsa gwamna na farko da ya gayyaci shugaban kasa ziyarar gidajen yari don nuna masa irin halin da suke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel