‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 30 a wasu kauyukan Zamfara biyu

‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 30 a wasu kauyukan Zamfara biyu

Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wasu sabbin hare-hare a kauyukan Dutsin Wake da Oho dake karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara tare da kasha mutane fiye da 30.

Saidai kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu, y ace mutane 10 ne ‘yan bindigar suka hallaka; 7 a kauyen Dutsen Wake da wasu 3 a kauyen Oho.

Harin ‘yan bindigar na jiya na zuwa ne cikin kasa da sati biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wani harin makamancin wannan a kauyen Zanuka dake karamar hukumar Anka tare da kashe mutane 23.

‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 30 a wasu kauyukan Zamfara biyu
Gwamnan Zamfara; Abdulaziz Yari

Ko kafin wadannan hare-hare, saida harin ‘yan bindiga a wasu kauyuka 10 ya tilasta daruruwan mutane dake masarautar Mada a karamar hukumar Gusau yin hijira.

Wasu mazauna yankunan sun shaidawa jaridar Daily trus cewar, ‘yan bindar na kai wadannan hare-haren ne a matsayin fansar daya daga cikin su da ‘yan bijilanti da aka fi kira da ‘yan sa-kai suka yiwa yankan rago bayan kama shi. Saidai shugaban ‘yan bijilantin ya shaidawa ‘yan bindigar cewar bashi da masaniya a kan mutanen da suka yanka dan uwan su.

DUBA WANNA: INEC ta haramta amfani da wayar hannu a wurin zabe, ta bayar da dalili

Majiyar Daily Trust ta shaida mata cewar, daga baya ‘yan bindigar sun samu labarin cewa wadanda suka kasha masu dan uwa ‘yan kauyukan Dutsen Wake da Oho ne.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Zamfara, Mista Kenneth Ebrimson, ya sanar da takwaran san a jihar Katsina cewar ,yan bindigar sun shigo dajin Ruggu dake yankin jihar ta Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel