A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram
A karo na farko mahaifiyar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau mai suna Falmata Abubakar tayi hira da muryar Amurka inda ta bayyana cewa ta kwashe a kalla shekaru 15 ba ta saka shi a idon ta ba.
Falmata Abubakar dai tana zaune ne a kauyen Shekau da ke Jihar Yobe, mahaifinsa limamin kauye ne amma ya dade da rasuwa.
Falmata ta shaidawa yan jaridar cewa a halin yanzu ba ta san inda Shekau ya ke ba kuma ba ta san ko yana da rai ko kuma ya mutu ba.
"Ko yana raye, ko ya mutu, ba ni da masaniya. Allah ne kadai ya san halin da ya ke ciki. Shekaru 15 kenan ban ganshi ba," inji ta.
Majiyar Legit.ng ta gano cewa mutanen kauyen Shekau ba kasafai suke fadawa mutane cewa garinsu daya da Abubakar Shekau ba saboda basu su son a rika danganta su da kungiyar ta'addancin na Boko Haram.
KU KARANTA: Yaki da Rashawa: Ingila za ta hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta
Mahaifiyarsa ta ce lokacin da ya ke karami, an tura Shekau Maiduguri don ya yi karatun addinin islama. A Maiduguri, ya yi rayuwa irin ta almajiranci kuma akwai yiwuwar ya yi bara a titunan Maiduguri kamar yadda sauran almajirai keyi.
Kamar yadda ta fadi, a lokacin da ya ke karatu a Maiduguri ne ya hadu da Mohammed Yusuf, wanda ya kirkiri Boko Haram bayan ya ayyana cewa karatun Boko kafirci ne. Falmata ta ce a lokacin ne aka sauya wa Shekau tunani.
Falamata ta cigaba da cewa tana son danta kamar yadda kowace uwa ke son danta sai dai halayensu sun sha banban a yanzu.
"Ya jefa al'umma da dama cikin bala'i, Ina na zan ganshi saboda in yi masa nasiha? Amma ina masa addu'a Allah ya shirye shi."
Falmata ta ce ba za ta tsine masa ba duk da cewa ya canja daga halayensa da ta sani kuma bata koya masa irin wadannan halayen ba.
Shekau da sauran yan kungiyar Boko Haram sunyi sanadiyar halaka rayyuka 30,000 da kuma sace mutane da yawa a yankin Arewa maso gabas da tafkin Chadi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng