Labari mai dadi: Marigayiya Hauwa Maina ta samu jika

Labari mai dadi: Marigayiya Hauwa Maina ta samu jika

Allah ya azurta jarumar fim marigayiya Hauwa Maina da samun jika daga yarta Maryam.

Rahotanni sun kawo cewa a lokacin da ake jimamin rasuwar Hauwa yarta Maryam Bukar Hassan ta kasance dauke da tsohon ciki.

Maryam ta haihu ranar Talata, 12 ga Yuni, 2018 a garin Kaduna, kuma ta samu da namiji wanda ke shike da koshin lafiya.

Labari mai dadi: Marigayiya Hauwa Maina ta samu jika
Labari mai dadi: Marigayiya Hauwa Maina ta samu jika

Ta bayyana wannan haihuwa a matsayin wani babban abin farin ciki da ya same ta a daidai lokacin da ta ke cikin jin zafin rabuwa da mahaifiyar ta.

KU KARANTA KUMA: An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza

A wani lamari na daban mun ji cewa rundunar yan sandan Minna, jihar Niger sun kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Shamsu Abubakar inda yake shiga irin ta mata yana damfarar maza.

An kama shi ne sanye cikin hijabi da zani, inda ya sha kwaliyya sannan yasa takalmi da jaka iri guda na mata.

Shamsu wanda ke zama a yankin Sayako hanyar Maitumbi, Minna, ya bayyana cewa ya dauki tsawon watanni yana wannan sana’a sannan kuma yayi nasarar damfarar maza da dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng