Yaki da rashawa: Kotu ta kwace naira biliyan 2.2 daga wajen wani babba a gwamnatin Jonathan
Wata babbar Kotun tarayya dake zamanta a garin Legas ta ta kwace makudan kudade da suka kai naira biliyan 2 da miliyan 200 daga wajen tsohon babban hafsan Sojan sama na kasa, Iya Mashal Adesola Amosu inji rahoton jaridar Channels.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin Kotun Mojisola Olatoregun ta yanke wannan hukunci ne bayan sauraron yin bukatar haka da hukumar EFCC ta shigar a gabanta,inda tace:
“Ina umartan Kotu ta kwace kudi N2,244,500,000 da hukumar EFCC ta gano a gidan Amosu da take zargin ya sata ne, ta mika su ga EFCC.”
KU KARANTA: Tsohon Gwamna da aka yanke masa shekaru 14 a gidan Yari yace duk yan Najeriya barayi ne
Haka zalika Alkalin ta kwace kimanin kudi naira milyan dari da casa’in (N190,828,978.15) daga hannun wani tsohon Daraktan kudi na hukumar Sojin sama, Olugbenga Gbadebo, da wasu kudi naira milyan 101 daga wani kamfanin Amosu ta mika ma EFCC.
Bugu da kari Alkali ta umarci EFCC ta wallafa dukkanin adadin kudaden da Kotu ta mika mata a manyan jaridun kasa guda biyu, don baiwa wanda ake kara ko kuma wani da yake ganin kudaden ba haramtattu bane ya zo gabanata ya bayyana mata hakan, kafin ta mallakama EFCC kudaden na dindindin.
Hukumar EFCC na tuhumar Amosu ne da wawurar kudi naira miliyan 663 daga asusun hukumar Sojin sama wanda yayi amfani dasu wajen siyan gidaje biyu a Landan. Haka zalika ya yi amfani da kudin hukumar wajen siyan gidan miliyan 900 a Legas, gidan miliyan 750 a Abuja, da sauran kadarori na biliyoyin nairori.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng