Madallah: Duba hoton wasu mutane 8 da dakarun soji suka ceto daga masu garkuwa a jihar Kaduna
A ranar Litinin da ta gabata ne dakarun sojin Najeriya dake atisayen Idon Raini domin kakkabe masu satar mutane da tayar da kayar baya suka yi nasar ceton wasu mutane 8 da masu garkuwa suka sace a kan hanyar Maganda zuwa Sofo a karamar hukumar Birnin Gwari.
Sojojin sun kwato mutanen ne yayin sintirin cigaba da kakkabe masu garkuwar da kuma aikata laifuka irin na ta’addanci a kan hanyar Maganda zuwa Funtuwa.
Daga cikin wadanda hukumar sojin ta kubutar yayin sintirin da take gudanarwa akwai maza uku (3), mata biyu (2), da kananan yara uku(3).
Darektan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chwukwu, y ace bayan mutanen da suka kubutar, sun yi nasar kwace wasu kayayyaki daga hannun masu garkuwar, da suka hada da; wata mota ja kirar Golf, Tirela, da kuma akwatunan kaya na matafiya.
DUBA WANNAN: Duba yadda wata motar alfarma ta rusa wani masallaci bayan ta kwace daga hannun direba
Kazalika, rundunar sojin ta ce, ta samu wani babur a kauyen Nachibi da mai shi ya gudu ya bari bayan hango ayarin sojojin na tunkaro inda suke aikata miyagun laifuka.
A kauyen Maidaro, dakarun sun fafata da wasu ‘yan binda da suka samu na gumurzu da wasu ‘yan kungiyar bijilanti yayin da suke kokarin sace shanu a kauyen.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng