Bagudu ya bayar da amincin Biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kebbi

Bagudu ya bayar da amincin Biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kebbi

Wani rahoto mai tattare da farin ciki da shafin jaridar The Nation ya ruwaito ya bayyana cewa, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya bayar da amincin sa na malalo kudade domin biyan albashin watan Yuni ga Ma'aikatan jihar sa.

Gwamnan ya bayar da amincewar sa ne domin biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikata na karkashin jiha da kuma kananan hukumomin dake fadin Jihar ta Kebbi.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sanarwa ta zo ne da sanadin Kakakin fadar gwamnatin jihar, Abubukar Mu'azu Dakingari yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin din da ta gabata.

Bagudu ya bayar da amincin Biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kebbi
Bagudu ya bayar da amincin Biyan Albashin watan Yuni ga Ma'aikatan Jihar Kebbi

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Dakingari ya bayyana wannan sanarwa ne da sanadin umarni na Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar Yauri.

KARANTA KUMA: Atiku da Jam'iyyar PDP sun yi Gargaɗi akan ɗaure Obasanjo

Alhaji Yauri yake cewa, gwamna Bagudu ya bayar da amincewar sa ne domin baiwa ma'aikatan jihar sa dama ta gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da annashuwa tare da iyalan su da 'yan uwa.

Ya kara da cewa, Gwamnan ya na kyakkyawan fata ga ma'aikatan jihar sa wajen gudanar da bukukuwan Sallah lafiya cikin farin ciki gami da annushuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel