Tsautsayi: Dakarun Soji Kasa sun salwantar da rayuwar Mai Jego, Jaririya da wasu Mutane 2 a Jihar Bayelsa

Tsautsayi: Dakarun Soji Kasa sun salwantar da rayuwar Mai Jego, Jaririya da wasu Mutane 2 a Jihar Bayelsa

Wata jaririya 'yar watanni shidda da haihuwa, mahaifiyar ta da wasu Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya yayin da dakarun Soji Kasa suka afka yankin Oluasiri domin gudanar da aiki a Karamar Hukumar Nembe ta jihar Bayelsa.

Kamar yadda shafin Jaridar The Punch ya bayyana, afkuwar wannan tsautsayi ta janyo cecekuce kan al'umma yankin dake gabar tafki a Kudancin Najeriya.

Majiyar rahotanni daga wannan yanki sun bayyana cewa, wannan lamari ya salwantar da rayuwar wani Mista Wilson Patason, Madam Beauty Christian da jaririyar ta 'yar watanni shidda da haihuwa da kuma wani mutum guda da ba a gano sunan sa ba yayin tattara wannan rahoto.

Wannan lamari ya afku ne a yayin da dakarun sojin suka afka yankin domin gudanar da aiki kan wasu tsageru da masu fashi a teku dake ɓoye a yankin na Oluasiri.

Tsautsayi: Dakarun Soji Kasa sun salwantar da rayuwar Mai Jego, Jaririya da wasu Mutane 2 a Jihar Bayelsa
Tsautsayi: Dakarun Soji Kasa sun salwantar da rayuwar Mai Jego, Jaririya da wasu Mutane 2 a Jihar Bayelsa

A yayin da wasu hukumomin tsaro suka yi ikirarin cewa dakarun sojin sun bude wuta ne a yankin sakamakon hari na harbin bindiga daga ake zargi na tsagerun ne, wasu mazauna yankin sun yi watsi da cewar dakarun sun bude wuta ne ba tare da wannan dalili ba.

Sai da wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, ko shakka ba bu akwai 'Yan Fashi na teku da Tsageru dake ɓoye cikin yankin ta karfi da yaji.

KARANTA KUMA:

Yake cewa, akwai yiwuwar rashin tausayi da tsananin mugunta ta tsagerun ya sanya suka bayar da sanarwar rahoton ta wannan fuska.

Cikin wata sanarwa ta al'ummar yankin da sanadin shugaban ta, Gamage Difurotogu, ta nemi gwamnatin tarayya da cibiyoyi masu kare hakkin dan Adam na kasar nan akan su gudanar a bincike na diddigi domin gano gaskiyar dake kunshe cikin wannan lamari.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Gwamnati za ta maida Gidajen Karuwai Makarantu a jihar Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel