Rushewar wani Gini ta salwantar da Rayuka 3 da raunata Mutane 7 a Garin Zaria

Rushewar wani Gini ta salwantar da Rayuka 3 da raunata Mutane 7 a Garin Zaria

Kimanin rayukan Mutane uku ne suka salwanta yayin da wasu mutane bakwai suka raunata a sanadiyar rushewar wani dogon Gini na Makaranta Islamiyya da ba a karashe ba na Unguwar Kaya dake Garin Zaria a Jihar Kaduna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan tsautsayi mai matukar munin gaske ya afku ne a ranar Juma'ar da ta gabata.

Yayin ganawa da Manema Labarai dangane da afkuwar wannan lamari, Mallam Abdul-Mumin Adamu, babban Sakataren Cibiyar bayar da agaji na gaggawa reshen garin Zaria ya bayyana wannan tsautsayi da abin takaici da kuma ban tsoro.

Rahotanni sun bayyana cewa, an samu nasarar ceto mutane bakwai wadanda suka raunata inda aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello dake garin Shika domin kulawa da lafiyar su cikin gaggawa.

Rushewar wani Gini ta salwantar da Rayuka 3 da raunata Mutane 7 a Garin Zaria
Rushewar wani Gini ta salwantar da Rayuka 3 da raunata Mutane 7 a Garin Zaria

Hakazakila an mika gawar mutane Ukun da suka riga mu gidan Gaskiya zuwa babban Asibitin inda aka kebance su a dakin ajiyar Gawa.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule

Shugaban Hukumar Kwana-Kwana na Jihar, Mista Paul Fedelix-Aboi ya bayyana cewa, bincike ne kadai zai iya tabbatar da musabbabin wannan tsautsayi da ya afku.

Yake cewa, duk da dai bayar da ceto da agaji na gaggawa shine nauyin da ya rataya a wuyan su, amma akwai bukatar al'ummar Kasar nan su daina neman rahusa da arha wajen gudanar da aikin gine-gine.

Mista Fedelix ya kuma shawarci al'umma akan neman kwararrun ma'aikata wajen tsayar ma su da gine-gine domin kawo karshen zagwayewar su a Kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne runduanr Sojin Kasa ta Najeriya ta samu nasarar sheke wasu 'yan ta'adda biyar a jihar Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng