Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda
- Jihar Kano da Katsina ne ke da kaso mafi yawa na matasa da su kayi nasarar a tantancewar da hukumar Yan sanda ta yi
- Jihohin da ke da karancin matasan da su kayi nasara sun hada da Abuja da Bayelsa da Gombe da kuma Ekiti
- Hukumar ta umurci wandanda su kayi nasara su hallarci gwajin lafiya da za'a gudanar tsakanin 31 ga watan Mayu zuwa ranar 3 ga watan Yuni.
Hukumar 'Yan sandan Najeriya ta fitar da sunayen wadanda su kayi nasarar cin jarrabawar tantancewa na farko da akayi, cikin mutane 37,000 da suka rubuta jarrabawar guda 5,253 kadai su kayi nasara.
Hukumar Yan sandan ta umurci wandanda su kayi nasara su hallarci gwajin lafiya da za'a gudanar tsakanin 31 ga watan Mayu zuwa ranar 3 ga watan Yuni.
KU KARANTA: Dalilin da yasa na zauna a bangaren 'yan jam'iyyar PDP - Dino Melaye
Jaridara Premium Times ta ruwaito cewa za'a dauki sabbin jami'an yan sandan ne daga kananan hukumomi 774 da ke kasar nan kamar yadda dokar gwamnatin tarayya ta tanada kamar yadda mataimakin Sufetan Yan sanda mai kula da horaswa Emmanuel Inyang ya bayyana.
Ga dai adadin mutanen da su kayi nasarar cin jarrabawar ta farko daga kowace jiha a Najeriya:
1. Abia - 114
2. Adamawa - 140
3. Anambra - 146
4. Bauchi - 133
5. Bayelsa - 54
6. Benue - 157
7. Cross River - 122
8. Delta - 166
9. Ebonyi - 91
10. Edo - 125
11. Ekiti - 84
12. Enugu - 119
13. Gombe - 75
14. Imo - 181
15. Kaduna - 161
16. Kebbi - 144
17. Kogi - 140
18. Kwara - 110
19. Lagos - 136
20. Niger - 169
21. Ogun - 140
22. Ondo - 125
23. Osun - 211
24. Plateau - 116
25. Rivers - 138
26. Sokoto - 161
27. Taraba - 112
28. Yobe - 110
29. Zamfara 99
30. Kano - 308
31. Katsina - 238
32. Oyo - 225
33. Akwa Ibom - 194
34. Borno -189
35. Jigawa - 189
A wata labarin, Legit.ng ta kawo rahoton cewa mutane masu sha'awan shiga aikin dan sandan a kalla 1,113 ne aka fara tantancewa a Legas a ranar 7 ga watan Mayu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng