Matashi 'dan shekara 19 ya sayar da kaninsa kan kudi N20,000 don ya biya sadaki

Matashi 'dan shekara 19 ya sayar da kaninsa kan kudi N20,000 don ya biya sadaki

Hukumar Yan sanda na jihar Neja sunyi ram da wani matashi dan shekara 19, Aliyu Basala Mohammed Yakutchi wanda ya sayar da kaninsa mai shekaru 6 ga wani mai suna Legbo da ke garin Afuwagi da ke karamar hukumar Mokwa wanda zai yi asiri da shi.

Bisala ya shaidawa jami'an Yan sandan SCIID cewa ya sayar da kaninsa Yamusa Ibrahim Yakutchi ga wani dan baranda kuma matsafi a kan kudi N20,000 amma fa bashi wanda ya ke sa ran zai yi amfani dashi wajen biyan sadakin budurwarsa Fatima mai shekaru 14.

Bisala ya shaidawa jami'an Yan sanda cewa shaidan ne ya rude shi har ya kai ga aikata wannan mumunan lamari inda ya kara da cewa a halin yanzu Legbo ya tsere tare da kaninsa duk da cewa bai biya shi kudin ba.

Matashi 'dan shekara 19 ya sayar da kaninsa kan kudi N20,000 don ya biya sadaki
Matashi 'dan shekara 19 ya sayar da kaninsa kan kudi N20,000 don ya biya sadaki

KU KARANTA: Auren wata mata ya mutu saboda juyawa mijin ta baya a shimfida

Da aka tambaye shi ko yarinyar da ya ke niyyar aura mai suna Fatima tana da masaniya a kan mumunan shirinsa na sayar da kaninsa don ya biya sadakinta, Bisala ya kada baki ya ce "Ni kadai na shirya wannan abu, Fatima bata san zanyi hakan ba."

Bisala ya shaidawa yan sanda cewa shi manomi ne kuma ya yi karatun islamiya lokacin yana yaro sai dai iyayensa basu da halin da za su tura shi makarantar boko kuma yaren Nupanci kawai ya iya.

A lokacin rubuta wannna rahoton wato jiya (Alhamis) 31 ga watan Mayu yan sanda basu yi nasarar gano wanda aka sayar wa yaron ba hakan yasa wasu ke juyayin cewa babu mamaki an kashe yaron ma.

Kakakin hukumar Yansandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa hukumar na yin duk mai yiwuwa don ganin cewa an kama matsafin wato Legbo tare da ceto karamin yaron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel