Kashi 70% daga cikin fursunonin dake jiran kotu ta yanke musu hukunci satar rake da doya suka yi – Abubakar Malami
- Abubakar Malmai ya ce kashi 70 daga cikin fursononi Najeriya kananan laifuka suka yi
- Minisatan Sharia da alkalin babban kotun tarayya dake Abuja sun kai wa gwamnan jihar Ribas ziyara a birnin Fatakol
Ministan sharia kuma babban Lauya kasa AGF), Abukakar Malami (SAN), ya bayyana cewa kashi 70% daga cikin fursunonin Najeriya dake jiran kotu ta yanke musu hukunci kananan laifuka suka yi kamar satar rake da doya.
Malami ya bayyana haka ne a lokacin da shi da alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Jastis Ishak Bello, da mambobin kwamitin rage yawan fursunoni a gidajen yarin kasar, suka kai wa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ziyara a gidan gwamnatin jihar dake birnin Fatakol.
AGF ya fadawa gwamnan cewa, an kafa kwamitin rage yawan fursunoni dake gidajen yarin Najeriya bisa umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda rage cunkoson fursunoni a gidajen yarin kasar.
Malami ya ce an sako fursunoni 126,500 bayan an biya taran da kotu ta ce a biya a kansu, kuma kwamitin ta fara yunkurin belin sauran fursunonin da taran su bashi da yawa.
KU KARANTA : Katin Mastercard da Visacard na Najeriya za su daina aiki a kasashen waje
Jastis Bello ya ce, gidajen yarin Najeriya sun cika sosai wanda ya sa fursonin da yawa basa iya barci saboda babu wurin kwanciya.
Gwamna Wike, ya fadawa kwamitin cewa cunkoson fsurunoni gidan yarin tarayya dake jihar Ribas ya zamo musu abun damuwa, shiyasa gwamnatin jihar ta fara yunkurin rage fursononin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?
Asali: Legit.ng